Buhari ya nada Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban EFCC.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattijai da ta tabbatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).
Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata.
Ya ce shugaban ya isar da bukatar hakan a cikin wata wasika da ya aika wa shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan.
Bawa, wanda ke da shekaru 40, yana daya daga cikin manyan jami’an hukumar EFCC daga shekara ta dubu biyu da biyar 2005.
A yanzu haka shine shugaban shiyyar hukumar yaki da rashawa. Kuma zai amshi mukamin ne daga hannun Mohammed Umar wanda ke aiki a matsayin shugaban jam’iyyar na rikon kwayar tun a watan Yulin 2020 bayan dakatar da Ibrahim Magu kan zargin cin hanci da rashawa.