Bayan harin Kagara, miyagu sun sake kai hari Neja, sun yi kashe kashe
Biyo bayan harin da miyagun yan bindiga suka kai kwalejin Kagara, jahar Neja, wasu miyagun sun sake kai farmaki karamar hukumar Shiroro inda suka kashe jama’a da dama.
Yan bindigan sun kai harin ne a kauyukan Sarkin Zama, Bakin Kogi, Siyiko da sauran kauyukan dake mazabar Gurmana, inda suka kwashe sa’o’i da dama suna cin karensu babu babbaka.
Shugaban kungiyar matasan Shiroro, Concerned Shiroro Youths, Sani Yusuf Kokki ya tabbatar da harin, inda yace yan bindigan sun kashe jama’a da dama, inji rahoton Daily Trust.
“Muna samun gawarwakin mutane bila adadin a kullum, wanda hakan yasa mutanenmu shiga mawuyacin hali game da tsaro.” Inji Kokki.
Sai dai duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin Kakaakin rundunar Yansandan jahar Neja, Wasiu Abiodun ya ci tura.