“Ba Gaskiya Ake Yadawa Ba Ina Nan Ban Mutu Ba ” -Tsohon Kwamishinan yan sanda CP Wakili
Labaran jita-jitar da aka fara yadawa a daren jiya Talata zuwa washe garin yau laraba.
Dakeccewa tsohon kwamishinan yan sandan jihar Katsina wanda daga baya ya koma Kano da kuma ya aje aiki a Kano wato CP Muhammad Wakili, ya tabbatar da cewa shi dai yana nan da ransa cikin koshin lafiya, bai mutu ba.
Tsohon Kwamishinan ya tabbatar da hakan ne a wata hira da ya yi da kafar sadarwa ta BBC Hausa a ranar Larabar nan.