An sace daliban sakandare masu yawa a jihar Neja
Rahotanni daga jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya na cewa wasu ‘yan bindigar sun afka wa wata sakandaren kimiyya ta gwamnati (GSC) da ke Kagara, inda suka yi awon gaba da dalibai da dama da kawo yanzu ba asan adadinsu ba.
‘Yan bindigar dai na sanye da kayan soji, kamar yadda jaridar PRNigeria ta ruwaito.
Majiyar daily episode Hausa ta ce yan bindiga sun mamaye harabar makarantar, sannan suka ci karfin masu gadin makarantar da ke da kimanin dalibai 1000 a daren Talata wayewar garin Larabar nan.
Ya zuwa yanzu ana ci gaba da kidaya sauran daliban da suka rage domin gane yawan adadin daliban da yan bindigar suka yi awon gaba da su.