Aƙalla sojojin Najeriya 10 ne suka mutu yayin wani artabu da mayaƙan ƙungiyar da ke da alaƙa da IS a Alagarno da ke Jihar Borno, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP.
Ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kai hare-hare guda uku a kan dakarun na Najeriya cikin wata sanarwa a jiya Talata, inda ta ce ta kashe sojoji bakwai ranar Litinin tare da kama wani guda ɗaya.
Wasu majiyoyin tsaro sun faɗa wa AFP cewa sojoji 10 ne suka mutu bayan dakarun Najeriyar sun kai wa sansanin ƙungiyar ISWAP hari ranar Litinin a Alagarno.
“Mun rasa soja 10 a faɗan kuma ‘yan ta’adda sun ɗauke ɗaya,” in ji majiyar. An kama sojan ne yayin da yake neman tsira sakamakon ruwan wutar da ‘yan bindigar suka yi musu, a cewarsa.
“An fafata sosai kuma an kashe ‘yan bindigar su ma, amma duk da haka sun rinjayi sojojin,” a cewar majiya ta biyu.
Mayaƙan ƙungiyar sun ƙwace mota huɗu da suka haɗa da motar silke da kuma na zirga-zirga.
Ƙungiyar ta wallafa wasu hotuna tana iƙirarin cewa sojan da ta kama ne da gawarwakin waɗanda ta kashe da kuma motocin da ta ƙwata daga hannunsu.
A cewar ƙungiyar, cikin ɗaya daga hare-haren da ta kai, ta yi wa sojoji kwanton-ɓauna a kan titin Gamboru zuwa Dikwa, inda ta kashe soja huɗu.
Garin Alagarno mai nisan kilomita 150 daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ya kasance matattarar ƙungiyar ISWAP, wadda ta ɓalle daga Boko Haram a 2016 kuma take cin gashin kanta.
Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 36,000 a yankin arewa maso gashin Najeriya, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.