Akwai Yiwuwar Zamu Rushe Gadar Ƙofar Nassarawa, Inji Gwamnatin Jihar Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ce akwai yiwuwar zata rushe gadar sama ta Ƙofar Nassarawa, tare da gina wata sabuwa.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Mallam Muhammadu Garba ne ya bayyana hakan, a yayin daya karɓi baƙuncin wata ƙungiya mai goyon bayan Gwamna Ganduje a ofishin sa.
“A halin yanzu gwamnatin Kano tana yin nazari akan yadda gwamnatin baya ta gina gadar Ƙofar Nassarawa, saboda haka akwai yiwuwar idan gwamnatin ta kammala nazari, zata ruguje gadar tare da gina sabuwa.” Inji Garba.