Ba Za A Iya Shawo Kan Matsalar Tsaro Ba, Ba Tare Da Hadin Kan Dilolin Man Fetur Ba.
Gwamnatin jahar Katsina ta gargadi dillalan man fetur da su guji sayar da man ga ‘yan ta’adda a jahar domin taimakawa wajen magance matsalar tsaro a jahar.
Jaridar “The Nation” ta ruwaito cewa, Mai Bai Wa Gwamana Aminu Masari Shawara a kan samar da man fetur da rarraba shi a jahar, Lawal Aliyu ya yi gargadin a lokacin wani taro da mambobin kungiyar dillalan mai ta kasa, IPMAN, reshen jahar wanda ya gudana a babban dakin taro na sakatariyar jahar.
Aliyu ya kara bayyana damuwarsa akan yadda wasu gidajen mai ke sayar da man ga masu taimaka wa ‘yan ta’adda ta hanyar daukar man su kai wa bata garin a cikin dazuzzuka.
Ya kuma yi korafin cewa, wasu direbobin tankokin mai na yin amfani da matsayinsu wajen daukar muggan kwayoyi daga wasu sassan kasar zuwa yankunan jahar masu wahalar shiga.
Mai bai wa gwamnan shawara ya ce, an kira taron ne da nufin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan yadda za su iya bayar da gudummuwa wajen dakile matsalar tsaro a jahar, inda ya kuma bayyana masu cewa, kwamitin ya mika wata bukata ga gwamnatin jahar ta a bai wa wasu karin gidajen mai da ke garuruwan kan iyakoki damar ci gaba da aiki.
Wakilai daga rundunar ‘yansanda da hukumar tsaron farin kaya su ma sun halarci taron.