Aiki na kyau: EFCC ta bankado makarantar koya wa matasa damfara a intanet a Abuja
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta bayyana samun nasarar bankado makarantar da ake koyawa matasa Sana’ar iya damfara a intanet.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar EFCC din Wilson Uwujaren shi ne ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai ranar Alhamis.
Ruhoton da jaridar Daily Episode ta samu na cewa anbankado makarantar, jami’in ya ce an bankado makarantar ne a yankin Mpape dake cikin birnin na Abuja.
Ya ce mafiya matasan da aka kama matasa ne da suka bar makaranta, kuma akwai mana da mata a cikinsu da shekarunsu bai wuce 18 zuwa 25 ba.
An kuma sami mota kirar Toyota Venza, da manyan wayoyin hannu 30, sai kuma kwamfutar hannu kwara daya.
Da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da su a gaban kuliya