Jagoran tawagar Lauyoyin Shehin Malami, Abduljabbar Nasiru Kabara, Barista Rabiu Abdullahi-Shuaibu ya shaida wa manema labarai a Kano cewa Sheikh Abduljabbar Kabara, ya kosa lokacin mukabalar da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya shirya yayi.
Abdullahi ya ce da kanshi ya tattauna da Shehin kuma ya tabbatar masa ya gama shiri tsaf domin gwabzawa da sauran malaman a wannan mukabala da gwamna Ganduje ya shirya da kansa.
Idan ba a manta ba Gwamna Ganduje ya amince a gwabza mukabala tsakanin duka malaman Kano da ke jayayya da Sheikh AbdulJabbar Nasir Kabara da su a bainar jama’ a a Kano.
Gwamna Ganduje ya ce duk wani malami da ke kalubalantar karantarwar Sheikh Abduljabbar ya je ya shirya a kowacce darika yake, Sunna, Salaf, Tijjaniyya, Kadiriyya, shiia da sauransu nan da makonni biyu za a goge raini a Kano.
Sannan kuma ya ce gwam ati za ta samar da wajen da za a gwabza da tsaro.
Gwamnatin jihar ta ce yin haka shine zai warware duk wata cece-kuce da ake ta yi tsakanin Sheikh Abduljabbar da sauran malaman kasar nan.
Gwamnatin Kano ta dakatar da Sheikh Abduljabbar daga yin karatu a Kano saboda katobara da ake zargin yana yi a addini. Hakan yasa har an rusa masa wani ginin makarantar sa sannan a saka jami’an tsaro su zagaye gidan sa.
Shigar da Kara
Lauyar Sheikh Abduljabbar ya ce sun shigar da kara babban kotu dake Kano domin a tilasta wa gwamnati ta janye jami’an tsaron da ta sa suka zagaye gidan malamin.
Sannan kuma da bi masa hakkin damar walwala da gudanar da addini kamar yadda doka ta ba shi dama.
Lauyan ya ce za a yi zaman sauraren shari’ar ranar 18 ga watan Faburairu.