A wani jawabi da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya fitar, fadar shugaba kasa ta ce duk wani sauran tasiri da PDP keda shi ya kare saboda ta zama jami’ar karya, wacce ta tara maƙaryata sannan ta cuci jama’a.
A cewar fada shugaban kasa, jam’iyyar PDP ba ta yi komai ba a tsawon mulkinta na shekaru goma sha shidda bayan assasa cin hanci da rashawa. Fadar shugaban kasa ta ce PDP ta bayar da kwangilolin bogi, na karya, domin kawai a wawure kudaden jama’a.
Wani bangare na jawabin ya bayyana cewa; “cin hanci ne ya jawowa jam’iyyar PDP faduwa zabe a shekarar 2015, wanda dukkanin kasar an san da haka, kuma tabbas shi zai cigaba da yi wa jam’iyya llla.
“Ita kuwa gwamnatin APC a karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta tsare kima mutuncinta. Ta samu nasarar murkushe cin hanci a fadar shugaban kasa, hakan ya sanya ‘yan Najeriya ke Allah san barka.
Jawabin ya bayyana cewa tasirin jam’iyyar PDP ya kare, mutuncinta tuni ya zube, Kuma ‘yan Nigeria ba zasu manta da irin ta’asar da suka tafka ba yayin mulkinsu.
Makaryacin da ya cinye amansa agaban dubbannin yan Nigeria wacce karyace bazai iyaba
Garba Shehu ka jira abinda Allah zaiyi maka game da isgilancin da kake tafkawa ga ‘yan Nigeria. Yaushe ka zama Boka mai duba?